A wannan karon ma an sami wasu da suka yi tsokacin yadda abin yake. Mahmud Lalo ya tattauna da daya daga cikinsu ta waya inda ya bayyana sunansa da cewa shine Yunana Shibkau kuma kakakin wata kungiyar hadakar kungiyoyin rajin kare dimukuradiyya da aiwatar da adalci ta Democracy and Justice wadda ke da mazauni a Birtaniya.
Shibkau ya bayyana cewa bukatarsu shine su ga an yi zabe an kare lafiya ba tare da wani tashin hankali ba sannan gwamnatin kasa ta sa matakan tsaro don a guji yadda zaben shekarar 2011 ya haifar da rasa rayukan mutane fiye da 800 guda sama da 8000 suka rasa matsuguninsu.
Da Lalo ya tambayeshi yadda suka ga yanayin zaben sai ya nuna sun zagaya tare da tarurruka a Arewacin Najeriya don ganin komai ya tafi lafiya cikin wayewar kai. Ya fadawa Muryar Amurka cewa ba su bada karfi a Kudancin Najeriya bane saboda a Arewa ne ‘yan siyasa suke amfani da addini da kabilanci wajen raba tunanin mutane wajen jefa kuri’a da kuma tursasa wa wasu zaben abinda bashi suka yi niyya ba.
Kuma ma a wancan zaben da ya gabata ba a sami wani rikicin a zo a gani ba a Kudanci. Daga karshe Yunana yace sun tattara rahoton bayanan abubuwan da suka tattaro don su gabatar ga wasu jami’an tsaro da kuma kafafen yada labarai.
Daga babban birnin tarayyar Najeriya ma wakilin Muryar Amurka Saleh Ashaka ya aiko mana da wasu hotuna masu dauke da wasu daga cikin masu sa idon da suka shika garin daga Kungiyar Tarayyar Turai.
Your browser doesn’t support HTML5