Malama Mansura Isa tsohuwar ‘yar fim kuma mai tallafawa mata domin su zamo masu dogaro da kai a yanzu, ta hanyar koya musu kananan sana’o’in dogaro da kai a yankunan karkara da ma wasu sassan burane.
Mansura ta ce kawo yanzu sun tallafawa kimanin mata dubu biyu, da sana’o’in domin su tsaya kan kafafunsu tare da basu jarin gudanar da sa’anar da suke sha’awa.
Ta kara da cewa daga cikin irin sana’o’in da suke koyawa mata sun hadar da dafa abinci, a cewarta shine sana’ar iyayenta hakan ce ma ya sa ta san sirin sana’ar tare da koya wa mata.
Baya ga sana’ar abinci ta ce tana koya wa mata sana’o’i irin su hada sabulu da omo, jaka ta mata sakar rigunan sanyi na yara, takalma da sauransu.
Malama Mansura, ta ce tana baiwa mata jarin dubu biyar biyar domin fara sana’a sannan sukan je su bibiye yadda matan ke tafiyar da harkokinsu, duk kuwa da cewar kudaden da take basu kyauta ne.
Ta kuma ce daga cikin kalubalen da suke fuskanta akwai matsalolin rashin hanya, mussamam ma kauyukan da ke cikin garin Kano, ko da yake ta ce basa samun matsala da su matan.