Wata tawagar masu bincike a Jami'ar Washington sun kirkiro wata manhaja ta wayar salula, wadda idan aka yi amfani da it tare da bututu na takarda, za’a iya gano ko yara sun kamu da ciwon kunne, zata taimaka wa iyaye su yanke shawara ko ya kamata su kai yaransu asibiti.
Wannan manhajar da aka bayyana ta a cikin mujallar kimiyya da fasaha a jiya Laraba, ita manhajar tana yin sauti irin na tsuntsaye, idan Iyaye suka yi amfani da bututun takarda aka saka cikin kunnen yara.
Ana kunna na’urar har na kimanin dakika 1.2, sa'an nan kuma tana amfani da sashen daukar sauti na wayar hannu, don saurarawa; zai shigar da sauti can cikin kunnen yara, wannan sautin shi zai gano ko kunnen ya kamu da ciwo.
Wannan Manhajar ta samu nasarar kashi 85% bisa dari, a lokacin da aka jarraba ta akan yara dari, wannan mahajar tana da tabbacin bada sakamako mai inganci, har fiye da gwajin amfani da ido da likitoci suke yi a Asibiti.