Wata kungiyar ‘yan kasuwa a kasar Kamaru sun kirkiro wata manhajar wayar hannu da za ta taimakawa manoma gano cututtukan dake kama amfanin gona. Haka kuma manhajar na bayyana matakan da ya kamata a dauka wajen magance matsalar da kuma hanyoyin da suka dace a bi don dakile matsalar.
Kamar wata al'ada ce ga Alanin Lietbou, a duk lokacin da ya ziyarci gonarsa, yana amfani da manhajar wayar domin ya duba lafiyar tumaturin da ya shuka. Manhajar na gano ko kayan gonan sun kamu da wata cuta. Da taimakon manhajar, manomin ya ce baya kashe kudi sosai kuma yana samun karin amfanin gona.
Lietbou yanzu yana amfani da manhajar da ake kira Agrix. Amfani da manhajar na da sauki. Kawai mai waya zai dauki hoton ganye ko 'yayan icce ne, daga nan sai manhajar ta yi nazarin matsalar dake tattare da shukar cikin ‘yan dakiku.
‘Daya daga cikin wadanda suka kirkiro manhajar Agrix, Dorothee Mvondo, ta ce har yanzu ana kan aikin bunkasa manhajar amma yanzu haka daruruwan manoma sun gwada amfani da ita.
Dorothee ta kuma ce tasirin da wannan manhajar za ta yi zai iya zama gagarumi. A cewar cibiyar kula da kayayyakin amfanin gona da kimiyya ta kasa da kasa, manoma a Afrika na asarar amfanin gona kimanin kashi 49 cikin 100 a duk shekara, wannan ita ce asarar kayan amfanin gona mafi yawa da ake samu a duniya.