Kungiyar kwallon kafa ta Manchester united ta lashe kofin nahiyar turai Europa league na shekara 2016/17
Manchester ta samu wannan nasarar ne sakamakon doke takwararta kungiyar Ajax a wasan karshe da ya gudana ranar Talata 24/5/2017 a kasar Sweden inda aka tashi wasan United tana da kwallo 2 Ajax tana Fafutuka.
Dan wasan Manchester na tsakiya Paul Pogba, shi ya jefa kwallon farko a ragar Ajax acikin mintuna na goma sha takwas da fara wasan. Daga bisani Henrickh Mkhitaryan, ya jefa kwallo ta biyu a mintuna na arba'in da takwas da wasan bayan dawowa daga hutun Rabin lokaci
Wannan shine karo na farko da Manchester, ta taba daukar wannan Kofi
Hakan kuma ya bata damar samun tikitin shiga gasar cin kofin zakarun turai UCL na shekara 2017/18 mai zuwa inda kungiyoyi biyar zasu wakilci Kasar Ingila a gasar ta cin kofin zakarun nahiyar turai
Kungiyoyin da suka fito daga Ingila sun Hada da Chelsea, Tottenham, Manchester City, sai kuma kungiyar Liverpool da Manchester united.
Your browser doesn’t support HTML5