Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tace zata dauko dan wasan baya na Chelsea David Luiz mai shekaru 30, da haihuwa a watan Janairu 2018.
Liverpool da Leicester City suna zawarcin mai tsaron baya na Westbromwich, Ahmed Hegazi, wanda yake kungiyar ta Westbromwich a matsayin aro daga Al Ahly na kasar Masar.
Watford ta Gargadi kungiyoyin Tottenham da Chelsea da su cere ransu wajan zawarcin dan wasanta mai suna Richarlison, dan kasar Brazil a watan Janairu domin bazasu sayar da shi a lokacin ba,
Swansea tana zawarcin dan wasan gaba na Liverpool mai suna Dominic Solanke, ita kuwa kungiyar Juventus da Liverpool, sun hade wajan neman dan wasan gefe na Sporting Lisbon, mai suna Gelson Martins.
Laurent Koscielny mai shekaru 32, da haihuwa na Arsenal ya ce zai kare taka ledarsa ne a kungiyar Lorient dake kasar Faransa,
Dan wasan gaba na Manchester city, Leroy Sane, ya ce kofar sa a bude take domin ya sake tsawaita zamansa a kungiyar a karshen kakan wasan bana.
Your browser doesn’t support HTML5
Haka shima dan wasan tsakiya na Manchester City David Silva, ya na daf da sabunta kwangilarsa a kungiyar zuwa 2020.
Manchester City, tace bazata sake dan wasanta Mangala, a watan Janairu ba sai dai dan wasan ya ce baya tsammanin zai sake dogon zama a kungiyar.
Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, tana neman ‘yan wasan masu amfani da kafar hagu wato (Left Footer) har guda hudu inda ta jero sunayen ‘yan wasan kamar, Gareth Bale na Real Madrid, Antoine Griezmann na Atletico, da Danny Rose, na Tottenham sai kuma dan wasan tsakiya na Arsenal Mesul Ozil.