"Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United na da nan da kwanaki 12 ta maido da tagomashin kungiyar," a cewar tsohon dan wasan ta Gary Neville.
Wadannan bayanan na zuwa ne bayan da Kungiyar ta sha kashi a karshen gasar Firimiya lig ta bana a makon jiya, a hanun masu jagoranci a teburin gasar, wato Liverpool wacce take kan ganiyarta a wannan lokacin da ci 2-0.
Hakan ya janyo ce-ce-ku-ce daga bangaren magoya bayan kungiyar, da su ka yi ta yiwa shugaban kungiyar Edward Wood kururuwa a lokacin wasan.
Wannan lamarin na zuwa ne yayin da dan wasan gaba na kungiyar Macos Rashpod, shi ma ya tafi jinya tsawon watanni 2 zuwa 3 sakamakon raunin da ya samu a wasa da suka doke Wolverhampton da ci 1-0 a gasar Kalu Bale na FA Cup.
Wasu na ganin jinyar dan wasan zata iya kawo koma baya wajen samun nasara a Manchester United matukar ba ta sayi 'yan wasa a watan Janairun nan ba.