Manchester City Da Chelsea Sun Haye

Manchester City da Chelsea

Kungiyoyin kwallon kafa guda takwas ne suka samu kaiwa ga zagaye na gaba wato (Round of sixteen) a turance na gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai UEFA Champions League na shekara 2017/18 bayan an tashi a wasannin da akayi ranar laraba 22/11/2017 na (UCL) a matakin wasan rukuni zagaye na biyu.

A cikin kungiyoyi talatin da biyu da suke fafatawa a gasar. kungiyoyin kwallon kafa na kasar Ingila suka fi yawa a cikin jerin sunayen kungiyoyi takwas da suka samu hayewa.

A kwai kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, sai Manchester City, da kuma Chelsea, Sai kasar Spain wacce take da Barcelona, da kuma kungiyar Real Madrid, wacce ke rike da kambun gasar.

Sauran sune hada da Paris Saint-Germain, ta kasar Faransa, sai Bayern Munich, daga kasar Jamus da kuma Besiktas daga kasar Turkiya.

A karshen wasan gaba na rukuni wanda kuma shine na karshe a wasannin rukuni na bana za'a sake zakulo kungiyoyi takwas da zasu cika su zamo kungiyoyi goma sha shida don gwabza wa a wasan kwab daya watau (Nock Out).

Your browser doesn’t support HTML5

Manchester City Da Chelsea Sun Haye - 4'32"