Manchester United Ta Bude Gasar Premier Da Nasara Akan Leicester

Dan wasan Man U. Paul Pogba, yana murnar cin kwallo.

Paul Pogba da Luke Shaw sun taimakawa kungiyar Manchester United wajen lashe wasan farko a gasar Premier ta Ingila, inda ta doke Leicester City da ci 2-1.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta fara gasar Premier ta Ingila da kafar dama.

Ta lallasa Leicester City da ci 2-1 a filinta na Old Trafford, a wasanta na farko, wanda har ila yau shi ne wasan farko a wannan kakar wasa ta 2018/2019 da aka fara bugawa a Ingila.

Kwallon farko ta zo ne daga Paul Pogba, wanda kasarsa Faransa ta lashe kofin duniya da aka kammala a Rasha a watan da ya gabata.

Pogba ya zira kwallon ne a minti na 3' sannan abokin wasansa, Luke Shaw ya kara wata kwallon a cikin minti na 83’.

An yi ta rade-radin cewa Pogba na yunkurin komawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.

Dan wasan Leicester City Jamie Vardy ya rama kwallo guda ga kungiyarsa a cikin zangon karin lokaci inda aka tashi a wasan da ci 2-1.