Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya kai ziyayar ba-zata a wani gidan man fetutur a yankin Apapa da Lekki inda ya musunta rahotannin da ke ta yaduwa akan gwamnati zata kara farashin man fetur, yana mai cewa rade-radin da ake ta bazawa ba su da tushe ballantana madafa.
Hukumar da ke kula da sa ido a tasoshi ko gidajen man fetur ta kasa, ta ce ta rufe gidajen man fetur da dama a dalilin kama su da shunku, ko kin sayar da man fetur din bayan su na da shi.
Yanzu haka babu dogayen layuka na jiran mai. Wakilinmu dake Jihar Legas, Babangida Jibrin, ya tattauna da wasu mutane da ke shan mai a wani gidan mai inda suka bayyana cewa sabanin makonnin da suka wuce, sukan tsaya a layin mai har maraice amma yanzu cikin mintoci uku zuwa hudu suka samu shan mai.
Mutane da dama sun yabawa gwmanati akan matakin da ta dauka na ganin cewa an samu wadatuwar man fetur, kuma sun samu sayan mai cikin sauki. Akwai alamun cewa duk wadanda suka sayi man fetur suka tara ko suka ajiye domin sayarwa don kazamar riba sun sayibogi, domin man fetur ya samu wadatuwa a Legas.
Ga cikaken bayani a rahoton Babangida Jibrin
Your browser doesn’t support HTML5