Mongi Hamdi ya bukaci kwamitin da ya gaggauta samarwa kasar ta Mali kudin da zata yi anfani da su wajen bunkasa samar da ruwan sha da inganta makararantu da kuma hasken wutar lantarki.
Yace samar da ababen more rayuwa ya zama wajibi, domin ko yanzu dubban 'yan gudun hijira da suka bar kasar za su fara kwararowa zuwa gida. Ya kara da cewa, kara gina ababen more rayuwa har sai yafi wahala bisa ga lalata su.
Kasar Mali ta sa hannu a wani shirin shiga tsakani da kasar Algeria ta shiga tsakaninta da 'yan tawayen abzinawa dama masu mara musu baya akan gwamnatin kasar, wadanda suke cewa gwamnatin kasar ta jinginesu a gefe kuma anyi biris da bukatunsu.
Sai dai ba wannan ne karon farko ba da aka kulla irin wannan yarjejeniar amma lamarin na sukurkucewa. A shekarar 2012 ne dai rikici ya balle a kasar ta Mali wanda yayi dalilin juyin mulkin da abzinawan suka kwace wasu muhimman birane a arewacin kasar kafin a fatattake su.