Mali: An Kashe Wasu Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya Na Majalisar Dinkin Duniya

An kashe jami’ai 5 daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya a Mali, wani mutum daya kuma ya jikkata sakamakon wani kwanton-bauna da aka yi masu jiya lahadi, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Harin ya faru ne a tsakiyar Mali yayinda sojoji daga Togo, wadanda ke cikin dakarun dake wanzar da zaman lafiya a Mali da ake kira MINUSMA a takaice, suke kan hanya, kusan kilomita 30 yamma da garin Sevare.

Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Sakatare Janar din Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon yayi Allah Wadai da harin a cewar mai magana da yawunsa, yana mai cewa ta’addanci ne babban barazana ga zaman lafiya da tsaron kasar.

Sakatare Janar din ya jajantawa iyalan jamai’an da suka rasa rayukansu wajen kokarin samar da zaman lafiya, don gwamanati da kuma al’ummar Togo, a cewar wata sanarwa daga Majalisar Dinkin Duniya.

Wani harin makamancin wannan ranar Jumma’a ya kashe sojojin Mali guda 5 tare da raunata wasu su 4 lokacin da motarsu ta bi ta kan nakiya a arewacin kasar bayan haka wasu ‘yan bindiga ruka bude musu wuta.

Adadin dakarun wanzar da zaman lafiya a Mali da suka rasa rayukansu a fagen daga bayan harin na jiya Lahadi, ya hau zuwa akalla 64, abinda ya sa ya zama mafi muni da Majalisar Dinkin Duniya ta taba gani.