Malaysia Ta Sauya Wasu Dokoki Dangane Da Daukar Baki Aiki

Wasu ma'aikata a kasar Malaysia

Kasar Malaysia, ta sassauta wasu ka’idoji da ta gindayawa ma’aikatun kasar wajen daukar baki a aiki.

Hakan na zuwa bayan da wasu kungiyoyin ‘yan kasuwa suka yi gargadin cewa matakin zai iya yin illa ga yunkurin da hukumomi ke yi na farfado da tattalin arzikin kasar da ya jikkata sanadiyyar annobar coronavirus.

Matakan kulle fita da hukumomin kasar ta Malaysia suka saka na tsawon watanni, sun taimaka mata wajen dakile yaduwar cutar ta COVID-19, amma kuma sun sa adadin marasa aikin yi, ya yi karuwar da a ba taba gani ba cikin gomman shekaru.

A karshen watan Yuli ne ma’aikatar da ke kula da daukan ma’aikata a kasar, ta ba kamfanoni masu zaman kansu umurnin su daina daukan baki aiki, a wani mataki na samarwa ‘yan kasar aikin yi.

Matakin da ya shammaci ‘yan kasuwa da dama, lamarin da ya sa suka yunkuro suka yi gargadin cewa, matakin ya yi hannun riga da kokarin da ake yi na farfado da tattalin arzikin kasar domin ma’aikatun na dogaro ne sosai da ma’aikatan da suka fito daga kasashen waje wadanda suke ayyuka marasa tsoka, wadanda aksarin ‘yan kasar ba sa son yi.

A dalilin haka, ma’aikatar ta sauya akalar tsare-tsarenta a makon da ya gabata, inda ta ba kamfanoni umurnin su ci gaba da daukan ma’aikata ‘yan kasashen waje, amma hade da wasu ‘yan tsauraran matakai da ta yi gargadi akansu.