Malaman Makaranta Zasu Fara Yajin Aiki Yau

A yau laraba ranar ce da majalisar dinkin duniya ta ware domin tunawa da Malaman makarantar boko, a fadin duniya.

Sai dai malamai a Nijar, sun ce za suyi zanga zanga, a yau domin yin Allah wadai da gwamnati dangane da kasa biyawa malaman bukatocin su, a daidai lokacin da dalibai ke komawa makaranta.

Malaman makaranta boko ‘yan kwantaregi sun kira dukkan magoya bayan kungiyoyin su a jamhuriyar Nijar, dasu gudanar da jerin gwano a dukkan hedkwatocin jihohin kasar domin nuna rashin jindadinsu dagane da irin halin kuncin rayuwan da suke ciki.

Malam Mustapha Abdulrauf, magatakardan kungiyar malaman makarantar, ya ce kungoyoyin sun tsara abubuwan da zasu gudanar na nuna Allah wadai da matakan Gwamnatin akan su a cikin wannan makon.

Ministan dake kula da ilimi a kasar Malam Dauda Marte, ya nuna irin kokarin da gwamnati keyi domin bunkasa karatu ta hanyar wadata makarantun da kayan aiki na biliyoyin SEFA, haka zalika da gina makarantun a inda babu su.

Your browser doesn’t support HTML5

Malaman Makaranta Zasu Fara Yajin Aiki Yau - 4'06"