Malaman Addini Sun Koka Kan Matsalar Amfani Da Ababen Sa Maye A Tsakanin Matasan Najeriya

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kungiyoyin fafatuka ke ta faman fadakar da jama'a akan illolin shaye-shayen kayan da ke sa maye.

A Najeriya a daidai lokacin da al'ummomi ke fuskantar matsalolin rashin tsaro, malaman addini na kira akan jama'a su koma ga ubangiji sai gashi wasu jama'a na ci gaba da aikata munanan ayukka wadanda kan iya kara jefa ‘yan kasa cikin halin kaka-nika-yi.

Wannan na zuwa ne lokacin da shaye-shayen abubuwan da ke sa maye ke ci gaba a cikin al'umma inda har jami'an tsaro basu tsira ga afkawa cikin ta'asar ba.

Rashin tsaro ne babbar matsalar da ke ciwa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya, sai dai tare da matsalar akwai wasu matsalolin da ke aaddabar jama'a wadanda ke kawo koma-baya ga ci gaban kasa.

An jima hukumomi na damke masu tu'ammuli da shaye-shayen kayan da ke sa maye a kasar amma kuma har yanzu matsalolin basu gadi karewa ba.

Alal misali a jihar Sokoto dake arewa maso yammacin kasar kwanannan ne mahukunta suka dira a wata unguwa wadda ta kasance maboya ga matasa maza da mata masu shaye-shayen kayan da ke sa maye da sauran sharholiya.

Faruk Abdulrahman Sayudi shugaban karamar hukumar Sakkwato ta kudu shi ya jagoranci samamen, ya kuma bayyana cewa tabbas sunga abuwawa da su ji dadin gani. Sun ga ana sayar da kwayoyin maye kala-kala, sannan har sun ga matasa hadda mata da ke ziyarta wurin don shaye-shaye.

Lokacin samamen an tarar da Jami'an tsaron ‘yan kasa na ‘civil defence’ na sa-kai da hannu dumu-dumu ga ta'asar da ake tafkawa wurin, abinda ya sa ma rundunar hukumar ta dauki mataki.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kungiyoyin fafatuka ke ta faman fadakar da jama'a akan illolin shaye-shayen kayan da ke sa maye.

Abubakar Mailato shi ne shugaban kungiyar rajin wanzar da zaman lafiya wadda ko a wannan mako ta gudanar da taron fadakarwa akan illolin shan kayan da ke sa maye.

Duba da cewa duk kokarin da hukumomi da kungiyoyi ke yi ga shawo kan wannan matsalar sun kasa magance ta.

Bisa la'akari da illolin da wannan matsalar ke haifarwa musamman wannan lokacin da wasu matsaloli suka dabaibaice Najeriya yin aiki da shawarwarin masana kan iya taimakawa ga samun mafita daga wasu matsaloli.