Malamaine Sanadiyyar Komabayan Ilimi

Yan makaranta

A wani bincike da aka gudanar a nan Amurka, me take “Hanyoyin da za’abi don bude kwakwalwar yara wajen fahimtar karatu” A cewar Ita dai marubuciyar, ta meda hankali ne wajen gano wai meke sa yara musamman ‘yan kasashen Afrika basu meda hankali wajen karatune? Tace a iya binciken da ta gudanar ta gano cewar wasu dalilai ne suke sa yara ‘yan makaranta basu maida hankali, wadannan dalilai ba wasu bane illa, yadda malamai basu nuna kishi a darussan da suke koyama yaran, mafi akasarin wadannan malaman sukan nuna halin ko oho ga wadannan daliban, wanda daga bisani yaran suma basu daukar karatun da wani mahimanci.

Ta kara da cewar, a cikin ilahirin bincike da ta gudanar, ta tagano wasu shika-shikan koyarwa, guda biyar. Wadanda tace idan aka bisu to bashakka za’a cimma nasara.

Na farko. Akwai bukatar malamai su nuna sha’awar su da damuwa a harkar karatu wanda tanan ne wadannan yaran za su yi kokarin suga sun zama kamar malamansu a rayuwa. Na biyu. Da akwai bukatar malamai su nuna ma yara mahimancin ilimi, don se da ilimi ne kawai zasu iya taimakama rayuwa wasu yaran.

Na uku. Akwai bukatar su luradda yaran mahimanci taimaka ma kasar su, ta hanyar zamowa masu ilimi. Se na Hudu, tagano bukatar da ake da ita na iyaye su dinga aiki hanu da hannu da malaman ‘yayansu.

Babban muhimi kuwa na karshe shine, gwamnatoci a kowane mataki su bama fannin ilimi matukar mahimanci da tabbatar da aiwatar da tsarin ilimin tilasa ga kowane dankasa, musamman a matakin Firamari da sakandire.