Malamai Sun Dukufa Neman Maslaha Kan Rashin Tsaro a Najeriya

Wasu daga cikin Malaman Addinin islaam da suka halarci taron a Abuja, Najeriya

A Najeriya, malaman addinin Musulunci na cikin gida da waje daga Mazhabobin Sunni da Shi'a 50 ne suka halarci wani taro na kokarin gano bakin zaren rashin tsaro da ma wasu dalilai da suka jibanci tashe-tashen hankulan jama'a ,musamman ma matasa saboda su ba da shawarwari ga mahukunta a kasar.

Malaman sun mayar da hankali ne kan matsalolin da suka kama daga ayyukan ta'addanci da sace mutane a yi garkuwa da su domin samun kudin fansa da ya ki ci ya ki cinyewa a jihohin Arewa irinsu Zamfara da Kaduna da Katsina da Jihar Binuwai kuma yake kokarin mamaye kasar.

Daya cikin Shugabanin Cibiyar yada kyakyawar fahimta tsakanin mabiya addinai, Mohammaed Nuraini Ashafa, ya ce hankalin kowa a tashe yake saboda rashin tsaro.

Shugabanin Musulunci sun fito su yi hobbasa wajen samo hanyoyi da za su taimaka wa mahukunta wajen magance matsalolin tsaron da ya ke addabar kowa da kowa.

Malaman sun fito da muhimman batutuwa 12 da a ganinsu ke haddasa rashin jituwa, da rashin yarda da juna a cikin al'umma, wadanda a cewarsu, su ne son zuciya, rashin gaskiya da kin neman sanin addini.

Shaihin Malami a fannin zamantakewa da zaman lafiya, kuma ba’amurke dan asalin kasar, Masar Farfesa Amir Abdallah, ya ce idan ana samun matsaloli da ke taba rayuwa da zamantakewan mutane, dole ne mutane za su nuna damuwa ta hanyar bijirewa da ka iya kawo tashin hankali a kasa, amma idan akwai fahimtar inda matsalolin suka samo asali za a iya dakile su.