A Jamhuriyar Nijar matan da ke koyar wa a makarantun firaimare sun bukaci shugabanin babbar kungiyar addinin Islama ta kasa da su shiga tsakani bayan da hukumomin ilimi suka sauya wa dumbin matan aure wuraren aiki.
A wani mataki na inganta harkar ilimi a yankunan karkara, hukumomi a Yamai sun sauya wa mata da dama wuraren aiki daga Birnin na Yamai zuwa yankunan na karkara.
A cewar matan wannan matakin zai iya bakanta rayuwarsu ta aure da kuma gurbata tarbiyar 'ya'yansu.
Hakan kuma ya sa daruruwan mata suka garzaya zuwa ofishin kungiyar addinin Islama ta IEN domin gabatar da wannan korafi.
A cewar Madam Madi Maryama Hassan, kakakin malaman mata, wadanda na kwantiragi ne, da farko an ce za a sauya wa wadanda ba su da aure ne wurin aiki kawai.
Ta kara da cewa, amma sai suka ga an jero sunayen mata masu aure a cikin sunayen wadanda aka tura karkara.
“Ba a bi sharuddan da aka ce za a bi ba wajen sauya wurin aikin.” Inji Madam Hassan.
Daga cikinsu da dama sun yi korafin cewa wannan mataki zai haifar da mutuwar aure, sannan zai shafi tarbiyar yara.
Shugaban kungiyar ta IEN, Sheikh Jabiri Isma’il, ya ce ya saurari sakon malaman, yana mai cewa “muma za mu gaya wa Allah kukanku.”
Ministan ilimi a matakin firaimare, Dauda Muhammadu Marte, ya ce, ba huruminsu ba ne su tsaya suna duba yanayi yadda iyalin ma’aikata su ke idan za a saka su aiki.
“Wannan ba a aikinmu ba ne.” Inji Marte yayin wata ganawa da suka yi da wakilin Muryar Amurka, Sule Mumuni Barma ta wayar tarho.
Saurari cikakken rahoton kan yadda zanga zangar ta gudana:
Your browser doesn’t support HTML5