Malamai a Nahiyar Afirka Na Bayyana Ra'ayoyin Su Gama Da Takun Saka Tsakanin Saudi Arabia Da Iran

  • Ladan Ayawa

Mideast Iran

Malaman addini islama na Shia da sunna a jamhuriyar Niger sun soma tofa albarkacin bakin su game da sabon salon da dangantaka ke dauka.

A cewar Malam Mammam Sani Ismaila mamba a mashabar Shi’a anan birnin konni kasashen Yamma ne ke tura kasar Saudi Arabia domin kawo tarnaki a gabas ta tsakiya musammam kuntatawa kasar Iran.

‘’Musammam idan kuka duba ina jin kafofin yada labarai daban-daban suna fadan irin abubuwan da suke gudana dama wannan azazzan abu ne kuma sai wannan abu ya zama kamar kishi maimakon a tsaya a gano me ke faruwa a gyara domin addinin yaci gaba to sai ana ta irin wadannan abubuwan.Musali ita Saudiyya tayi ta takale-takale gabanin wannan kissan taso Iran .

Ga Haruna Mamman Bako da Karin bayayi

Your browser doesn’t support HTML5

MALAMAI A NAHIYAR AFRICA NA BAYYANA RAAYOYIN SU GAME DA TAKON SAKA TSAKANIN SAUDI ARABIA DA IRAN 2'06