A wannan mako Dandanlinvoa ya leka karkara ne inda muka zanta da Hauwa Isyaku, mai sana’ar koli-koli daga karamar hukumar Tofa, kuma ta yi cikakken bayani dangane da sana’ar ta da kuma irin alfanun da take samu.
Malam Hauwa, ta ce babban abinda ta fi shi’awa shine sauran masu karamar sana’a irin tasu su kafa kungiya domin masu ire-iren sana’ar su zama karkashin inuwa daya wajen kai kokensu ga mahukunta tare da sama musu maslaha da hanyar cigaban sana’ar ta su.
Malama hauwa ta bukaci masu hannu da shuni da su sanya jari a sana’ar koli-koli da man-gyada, kuma a cewar ta sakamakon dimbin ribar da ke tattare da sana’ar, babu shakka kwalliya zata biya kudin sabulu.
Ta kuma kara da cewa sana’a ce da mai karamin karfi zai iya farawa sannan mai babban jari kuwa ya kwashi riba mai yawa. Daga karshe malama Hauwa ta ce matsalar da suke fuskanta itace, idan aka sami gyada mara kyau, bata fidda mai sannan ba’a samun riba idan akayi rashin sa’a.
Your browser doesn’t support HTML5