Rahotanni daga Najeriya, na cewa fitaccen mahaddacin Al Qur’anin mai girma, Alaramma Malam Ahmad Ibrahim Suleiman ya kubuta, bayan garkuwa da aka yi da shi na kusan makonni biyu.
An yi garkuwa da Malam Suleiman ne a yankin jihar Katsina a lokacin yana kan hanyarsa ta komawa Kano.
Daya daga cikin surukan malamin, Isma’ila Maiduguri ya bayyanawa Muryar Amuka cewa shehin malamin ya kubuta.
“Matata (diyar malam) ta yi waya da su, duk gidan an yi waya da su.” Inji Isma’il.
Ya kuma kara da cewa, ba a biya kudin fansa ba, yana mai cewa “a cikin daren nan ne Allah ya sa suka kubuta wallahi ba tare ma da ko sisi ba.” Isma’il ya kara da cewa.
Surukin na malam bai yi cikakken bayani kan yadda malamin ya kubuta ba.
Wadanda suka yi garkuwa da malamin sun nemi kudin fansa har Naira miliyan 300 amma Isma’il ya ce an yi musu tayin naira miliyan 30, wacce ma ba a kammala hada ta ba.
Matsalar garkuwa da mutane a Najeriya ta zama ruwan dare, musamman a yankin arewa maso yammacin kasar.
Saurari cikakkiyar hirar Nasiru Adamu El Hikaya da surukin malam, Isma'il Maiduguri:
Your browser doesn’t support HTML5