Makiyaya da Manoma Sun Yi Taron Neman Sulhu

'Yansandan Najeriya

Zaman sulhun ya gudana ne a birnin Umuahia babban birnin jihar Abia.

Taron da aka shirya a karkashin rundunar 'yansanda ya samu halartar wakilai daga jihohin kudu maso gabas da kudu maso kudu.

Bisa ga duka alamu an soma samun masalaha kamar yadda shugaban kwamitin da babban sifeton 'yansanda Suleiman Abba ya kafa, wato mataimakin sifeton 'yansandan AIG Usman A Gwari. AIG Gwari yace bangarorin guda biyu na kowane jiha suna da kwamiti. An kira bangarorin biyu daga kowace jiha a zauna dasu.

A zaman da aka yi dasu sun bayyana damuwarsu. An yi yarjejeniya a rubuce. Kana masu gona sun ce nan gaba ba zasu dauki doka a hannunsu ba. Idan Fulani sun shiga gonakansu zasu kai kara. A kowace jiha akwai kwamiti da ya kunshi Fulani da manoma da zasu jagoranci kowace jiha.

Wakilan Fulani da manoma a wurin taron sun bayyana korafe-korafensu. Wani yace yawancin lokuta Fulani na shigowa kauyukansu da bindigogi da adduna kana kuma su ci zarafin matansu. Amma yunda magana ce ta sulhu da shigowar 'yansanda suna marhabin da hakan.

Alhaji Gidado Sidiq shugaban Miyetti Allah reshen jihar Anambra yace matakin da aka dauka zai kawo karshen damuwar da suke fuskanta.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Makiyaya da Manoma Sun Yi Taron Neman Sulhu -3' 57"