Makamai Suna Kara Korara a Yankin Niger Delta

Makamai da albarusai da sojojin Najeriya suka ce sun kama daga hanun 'yan binidga. (File Photo)

Rundunar 'Yansanda a jihar Rivers Ta koka kan yawan makamai da suke kara shiga hannayen mutane da hakan ya saba ka'ida.

Kasa da wata daya kamin a fara zaben kasa a Najeriya, hukumomin tsaro suna kara zage dantse domin maganin masu neman tada zaune tsaye. Duk da haka hukumomin tsaro musamman ta 'Yansanda a jihar Rivers, ta koka kan yawan makamai da suke kara shiga hanun mutane ta hanyoyin da suka kaucewa doka.

Kakakin rundunar 'Yansandan jihar DSP Kidaya Mohammed, yace rundunar tana samun gagarumin nasara wajen kwato makamai daga hanun mutane da basu dace su mallake su ba. DSP Mohammed, yace ko wadanda aka baiwa lasisin mallakar makamai, an basu umarnin su maida su ga ofisoshin 'Yansanda.

Daga nan yace tana samun nasara wajen takawa barayi cikin teku birki, kan irin barnar da suke yi, al'amari da yake shafar tattalin arzikin Najeriya.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Makamai Suna Kara Korara a Yankin Niger Delta