Masu bincike sun kiyasta cewa makamai kimanin miliyan goma ne ke yawo a kasashen yammacin Afirka wadanda suka shigo ta barauniyar hanya.
Barayi da 'yan fashi da masu satar mutane da 'yan ta'adda, irinsu Boko Haram,ke yin anfani da makaman domin aikata danyan aiki.
Yin la'akari da tashin tashinar da kasar Nijar ke fuskanta saboda wadannan makamai dake yawo barkatai suna fadawa hannun mugayen mutane, ya sa hukumomin kasar suka shirya taron horas da jami'an tsaro akan yadda zasu gano su kuma su kwato irin wadannan makaman. Taron ya koya masu dabarun tantance makaman.
Kwamandan jami'an, Tsalha Muhammad yace idan suka kama wani da yayi aikin asha da makami zasu duba lambar makamin da asalin kasar da aka kerashi ko kuma su aikawa masu binciken makamai na kasa da kasa domin samun cikakken bayani da kuma bayyana abun da aka yi da makamin.
Binciken zai nuna lokacin da aka kerashi da kuma kasar da aka sayarwa. Daga nan sai su tambayi kasar da aka sayarwa ta bayyana yadda makamin ya fita daga hannunta.
Alkalan shari'a na cikin wadanda suke daukan horon. Ali Isa Jibo na kotun Yammai ya bayyana irin hukuncin da doka ta tanada wa wanda aka samu da bindiga ba bisa kan ka'ida ba. Yace duk wanda aka kama haka ana iya yi masa hukuncin daurin shekara biyu zuwa goma tare da tara.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5