Majalisun Tarayyar Najeriya Zasu Koma Aiki Gobe

Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Yau hutun sallah da 'yan majalisun tarayyar Najeriya suka dauka ya kare. To wadanne irin matsaloli ne zasu dauke hankalinsu yayinda suka koma bakin aiki yau?

'Yan Najeriya sun sha yin anfani da shafukan zumunta ta yanar gizo wajen yin muhawara akan yadda gurfanar da shugaban majalisar dattawa ka iya shafar danfantaka tsakanin majalisar da bangaren gwamnati.

Sanata Ibrahim Kabiru Gaya ya yi tsokaci akan lamarin. A nashi ganin mutane ne ke neman mayarda batun na siyasa. Yace suna goyon Shugaba Buhari bisa ga tuk tsarin da yake kawo masu. Ashirye suke su ba shugaba Buhari goyon baya dari bisa dari domin ya sami yadda zai gyara kasar..

Shugaba Muhammad Buhari gwarzo ne kuma mai kishin kasa saboda haka kowa ya kamata ya bashi hadin kai domin ya yiwa kasa aiki, inji Sata Gaya.

Batun gurfanar da shugabansu Bukola Saraki yace mutane ne suke maganganu iri iri sun mayar da abun siyasa.

Abun da kuma ya dauki hankalin masu muhawarar shi ne kudaden da aka ce 'yan majalisa sun kwasa gabanin zuwa hutunsu. Wata jarida ta ce kowane sanata ya karbi nera miliyan ashirin da daya da rabi kana na majalisar wakilai ya karbi nera miliyan goma sha bakwai da rabi.

Wasu masu sharhi sun ce kudaden sun yi yawa. Amma Sanata Abdullahi Adamu da yake magana akan kudadensu yace an rage albashinsu da alawus zuwa rabi kamar yadda aka bayyana.

Ga rahoton Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisun Tarayyar Najeriya Zasu Koma Aiki Yau - 2' 57"