Majalisun Dokokin Amurka Sun Ce Amurka Bata Takawa Rasha Birki

Shugaban Amiurka, Barack Obama

Wakilan majalisar dokokin Amurka sun bayyana damuwa cewa, kamar gwamnatin Obama bata daukar matakai na taka birki kan abunda suka ce muguwar rawar da Rasha take yi a kasashen Ukraine da Georgia.

"Na damu cewa, sakon da shugaban Rasha Vladimir Putin yake dauka daga irin matakai da muke dauka shine irin takalar da yake yi mataki ne da ya dace," inji Senata Bob Menendez.

Maganar da 'yan majalisar suke yi shine kama zirin Crimea da Rasha tayi a shekara ta 2014, da kuma ci gaba da goyon bayan d a take baiwa 'yan tawayen gabashin Ukraine.Haka nan a shekara ta 2008, Rasha tayi amfani da karfin soji a kasar Georgia, daga bisani ta goyi bayan ballewar kudancin Ossetia, da Abkhazia, a zaman kasashe masu zaman kansu.

"Me yasa bama amfani da madafun difilomasiyya masu karfi, wadanda zasu taimaka mana watakil Rasha ta gane cewa, akwai ranar kin dillanci kan irin matakai d a take dauka, inji Senata Menedez, a zaman kamitin majalisar dattijai kan harkokin waje.

Amma da take kare gwamnatin Obama, kan batun na Rasha, mukaddashiyar sakataren harkokin wajen Amurka mai kula da sashen Turai da kuma Asiya, Victoria Nuland tace, Rasha ta dandana kudarta a karkashin takunkumin da Amurka da kawayenta suka azawa Rasha saboda wadannan matakai, wadanda suka hada da takunkumi kan kadarori da kuma na hana jami'an Rasha walwalar tafiyer tafiye.