Kwamitin an kafashi ne da nufin cewa kasar Najeriya ta shiga jerin kasashen duniya da zasu yaki cutar shan inna kuma su kawar da itadaga kasashensu.
Bayan an saurari rahoton da yin nazari akai gwamnatin kasar tayi na'am dashi cewa an samu gagarumar nasara saboda daga mutane 43 dake dauke da cutar da suka fito daga jihohi tara bara, yanzu shida kawai suka rage daga jihohi biyu. Jihohin biyu su ne Kano da Yobe. Ana zaton kafin karshen shekara za'a gama da cutar baki daya.
Ministan kiwon lafiya Dr. Haliru Alhassan wanda ya jagoranci kwamitin yayi karin haske. Yace ba gwamnatin Najeriya ba kawai har da majalisar dinkin duniya da kasashe masu hulda da Najeriya sun yaba da rawar da kasar ke takawa wajen kawar da cutar. Kawo yanzu an samu jihohi a arewa da basu da cutar cikin shekaru ukun da suka gabata. Idan an dore haka zuwa karshen shekara z'a kawar da cutar.
Dangane da cewa ana yawan yiwa yara allurar lamarin da wasu ke ganin akwai wata manufa sai ministan yace ba haka ba ne. Ita cutar shan inna kashi uku ce. Shi ma maganin yana da sinadari kashi uku. Idan an ba yaro maganin to ko cutar ta kamashi bayan ya girma jikinsa zai kasheta kuma ba zata yi masa la'ani ba.
Akwai wata allurar da mace na iya karba lokacin da take da juna biyu. Wannan allurar zata yiwa dan da ta haifa kariya na wata shida zuwa tara da haihuwa kafin ta daina aiki. Sai dai ba'a san lokacin da zata daina aiki ba. Cikin wannan lokacin ko an yiwa yaron allurar rigakafi ba zata yi masa aiki ba. Dalili ke nan da yasa a keyin allurar akai-akai. Bata da wata cuta saidai ta bada kariya.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5