Majalisar Wakilan Najeriya Na Gani Ya Kamata A Ba Masana'antu Tallafi

A Kokarin ganin an farfado da masana'antun da suka dade a durkushe, bangaren majalisar wakilan Najeriya da gwamnati sun ce za a bi hanyoyi daban daban don farfado da masana'antun domin bunkasa tattalin arzikin kasar.

Majalisar wakilan Najeriya ita ce ta fara bayyana bukatar a farfado da masana'antun domin samar wa matasa ayyukan yi, duk da cewa yawancin matasan sun riga sun rungumi noma a matsayin sana'a.

Dan majalisa mai wakiltar Koko Bese da Mayama a Jihar Kebbi, Shehu Mohammed Wamban Koko, shi ne ya fara gabatar da kudurin a gaban majalisar wakilai, inda ya ce ya tuna da wasu kamfanoni da ke yin lemon kwalba a jihar sa a shekarar aluf dari tara da cisi’in da hudu amma yanzu babu su, sannan ya kawo bayanin wasu masana’antu da ya ce yana ganin koma bayan tattalin arziki da aka samu a kasar ne ya kawo durkushewarsu, shi ya sa ya gabatar da kudirin bukatar a basu tallafi saboda a yi wa tattalin arzikin kasar garambawul gaba daya.

Amma Sanusi Maijama’a Ajiya, mataimakin shugaban kungiyar masu masana'antu da aikin gona ta kasa, ya ce tallafi bashi ne. Saboda haka ya kamata a zauna da gwamnati, da ‘yan majalisar dokokin kasar, tare da masu ruwa da tsaki a tambayesu abinda suke so kafin a yanke wannan hukuncin. Domin abinda ya ke gani shi ne a fara samar da kayayyakin da masana'antun ke bukata tukuna, kamar wutar lantarki da injina kafin a kai ga maganar bada tallafi, domin tallafi bashi ne kuma ba kowa ne yake son bashi ba.

Shi kuwa, Ministan Noma da raya karkara Sabo Nanono, ya bada tabbacin cewa masana'antu na daga cikin jiga-jigan ayyuka guda 3 da gwamnatin Najeriya ta shirya farfado da su cikin gaggawa, duba da yadda a shekarun baya kayayyakin da suke sakawa na daya daga cikin wadanda suka fi inganci a nahiyar Afirka baki daya, saboda haka za a ba masu zuba jari daga kasashen waje dama domin su taka rawa a wannan fannin.

Ga karin bayani a cikin sauti daga Medina Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Wakilan Najeriya Na Gani Ya Kamata A Ba Masana'antu Tallafi