Majalisar Wakilan Najeriya Ta Kalubalanci Jami’an Tsaro Kan Matsalar Garkuwa Da Mutane A Abuja

Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps)

Majalisar ta ba da wa’adin makonni uku don kammala binciken a kuma gabatar mata da rahoto kan lamarin.

Majalisar Wakilai ta umarci kwamitocinta na Babban Birnin Tarayya (FCT), 'Yan sanda da su gudanar da cikakken bincike game da yawaitar sace-sace da fashi da makami a babban birnin kasar.

Majalisar ta ba da wa’adin makonni uku don kammala binciken a kuma gabatar mata da rahoto kan lamarin.

Babban birnin na Najeriya a ‘yan shekarun bayan nan na fuskantar matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane.

A cikin wani kuduri na gaggawa, Wakili Ismail Dabo ya nuna bakin cikin kisan wata mataimakiyarsa, Nimah Sulaiman, wadda aka yi wa kisan gilla bayan da aka dauke ta a motar haya ta “One Chance” kusa da Bannex Junction a yankin Wuse na Abuja a ranar Alhamis din da ta gabata.

Yayin da aka yi shiru na minti daya domin tunawa da marigayiyar, majalisar ta yi Allah wadai da sake bullar ayyukan masu motocin haya na 'One chance' tare da yin kira ga hukumomin tsaro da su kawo karshen wannan matsala.