Yunkurin da gwamnati tayi ta hanasu shiga zauren majalisar domin su yi taronsu ya sa sun yi anfani da karfin tuwo inda suka balle kofar shiga kafin shugaban majalisar ya samu shiga.
Jajircewar 'yan majalisar, duk da barkonon tsohuwa da 'yansanda suka dinga jefa masu, ya sa sun samu sun yi zaman sa'o'i biyu.
Kafin su watse sun ki su sake duba bukatar shugaban kasa akan sake sabunta dokar ta baci a jihohn Borno, Yobe da Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya. Maimakon haka ma sun fara shirin tsige shugaban ne.
Oanarebul Sha'aibu Gwanda Gobir yace sun fara sa takardar tsigewa ko korar shugaban kasa domin ya kasa tsare tsarin mulkin kasar. Shugaban ya kasa kare 'yan Najeriya daga hare-haren Boko Haram. Shugaban ya rage darajar kasar a idon duniya. Bai cancanta ya shugabanci jama'a ba. Idan yana son ya zama shugaban Ijaw sai ya je ya zama shugaban Ijaw din.
Yadda jami'an tsaro suka kutsa harabar majalisar ya kasance abun damuwa ga 'yan majalisar da dama. Yin hakan katsa landan ne ake yiwa dimokradiya.
Yanzu dai dokar ta baci ta sha ruwa domin ta kare yau saidai shugaban ya sake tuntubar majalisar da wata wasika.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5