Daga dukkan alamu wata sabuwar rigima za ta kunno kai tsakanin fadar gwamnatin Tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da kuma majalisar kasa wadda ke karkashin jagorancin Dr. Bukola Saraki dangane da kudurin tsarin zabe da majalisar ta aika wa shugaba Buhari ya saka hannu akai amman ya yi kememe ya ki saka hannu kuma ya maida wa majalisar kamar yadda dokokin Najeriya suka tanada.
Tsarin zaben da hukumar zaben Najeriya ta gudanar majalisar bata amince da shi ba inda majalisar ke son ayi zaben shugaban kasa a karshe sabanin yadda hukumar zaben Najeriya ta tsara cewa za a yi zaben shugaban kasa da farko tare da na 'yan majalisa.
Babban jami'in hulda da manema labarai a fadar gwamnatin Najeriya Malam Garba Shehu ya bayyana hujjojin da shugaban ya gabatar wa majalisa akan dalilin kin kudurin da suka kawo masa, inda ya ce ana zargin akwai siyasa a ciki, ya kuma bayyana cewa an saba wa tsarin mulki kuma shugaban ba zai yi abin da ya saba wa tsarin mulkin ba.