Majalisar Koli Ta Musulmin Najeriya Ta Kaiwa Shugaban kasa Korafi

Sarkin Musulmi Mai Martaba Sa'ad Abubakar

Majalisar koli ta Musulmin Najeriya tayi korafi akan kujerun wakilci da aka baiwa Musulmi a taron kasa.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, yayi alkawarin cewa zai dauki matakai na kawo gyara akan koken da kungiyar majalisar koli ta Musulmin Najeriya tayi a lokacin da suka kai masa ziyara a karkashin jagoranci Sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar.

Wannan korafi dai na cewa musulmi suna ganin cewar an kwaresu a wurin raba kujeru na wakilci a taron kasa da ake gudanarwa a Abuja.

A wani hira da wan lauya Mainasara Umar yayi da wata kafar yada labarai a Abuja, yace lallai wanan ziyarar da majalisar musulmi ta Najeriya ta kai fadar gwamnati tamkar ta makaro.

Yace suna kasar ne aka fidda sunayen wadanda zasu je, suna kasar na aka fito da jadawalin alkallumar cewa daga cikin mutane dari hudu da tamanin da biyar da zasu je taron, kashi sittin da biyu kirista ne, kashi talatin da takwas ne musulmi.

Ya ci gaba da cewa suna kasar ne aka fara taron nan, suna kasar ne aka fara taron da mahawara mai zafi kan maganar addini, saboda shugaban taro ya bude taro da assalamu alaikum.


Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Koli Ta Musulmi Najeriya -4'35"