Majalisar Kano Ta Yi Karatun Farko Kan Kudurin Dokar Sabbin Masarautu

Hotunan bukukuwan hawan Nassarawa da aka gudanar a kanoa shekarar 2018

Yau majalisar dokokin jihar Kano ta karbi rahotan kwamitin da ya yi nazarin akan kudin dokar kula da ayyukan majalisar masarautar Kano wadda ya kunshi batun kirkiro da sabbin masarautu guda hudu.

Rahotan kwamitin wanda shugaban masu rinjaye na majalisar Hon. Baffa Babba Dan Agundi ya karanta a zauren majalisar ya yi nazari game da tarihi da kuma sassan gundarin dokar kula da aikace-aikacen majalisar masarautar Kano.

"Na farko rahoto ya amince cewa a yi karin sakaruna guda hudu, Gaya Rano, Karaye, Bichi zuwa masu daraja ta daya." Inji shugaban kwamitin, Hon. Baffa Dan Agundi.

A yayin zaman majalisar na yau, daruruwan mutane ne daga yankunan da ke muradin kirkiro masu sabbin masarautu.

"Mun zo ne mu nuna goyon bayan bisa wannan yunkuri da gwamntin jihar Kano na bada babbar masaruata a karamar hukumar Rano." Inji Ado Bello na Annabi, wanda na daya daga cikin dinbin matasan da suka yi dafifi a harabar majalisar.

Haka zalika, dinbin wakilai ne daga lardin Gaya masu muradin a kirkiro masu masarautar Gaya suka yi Dandanzo a majalisar a yau.

"Jama'a ne suke bulbulo suke neman biyan bukatarsu, domin tarihi ne yake maimaita kansa." A cewar, Malam Nura Kani Gaya shine Danmasanin Gaya a yanzu.

Bayan karbar rahotan, majalisar ta yi karatu na farko akan daftarin dokar kirkiro da sabbin masarautun da kuma ayyukan masarauta a Kano.

A gobe ne ake sa ran wakilan majalisar za su ci gaba da aikin akan daftarin.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano ta farfado da aikin binciken almundahana kan yadda aka sarrafa kudaden lalitar masarautar Kano tun daga shekara ta 2013 zuwa bara.

Yanzu haka dai hukumar ta aike da takardar gayyata ga tsohon sakataren majalisar masarautar Kano Malam Isa Bayero dangane da wannan bincike.

Yunkurin samun karin haske game da dalilan farfado da wannan aikin bincike daga shugaban hukumar, Muhuyi Magaji ya cutura saboda baya gari.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano:

Your browser doesn’t support HTML5

Kano: Majalisa Ta Yi Karatun Farko Kan Kudurin Sabbin Masarautu - 3'27"