Majalisar Dokokin Iraqi ta yi kira ga gwamnati a jiya Lahadi cewa ta kori dakarun Amurka dubu 5,200 daga kasar domin kalubalantar harin da Amurka ta kai da jirgi marar matuki da ya kashe babban sojan Iran a filin saukar jirage na Bagadaza.
Majalisar Dokokin mai rinjayen Shi’a ta kada kuri’a a kan kudurin dake kiran gwamnatin wucin gadin ta kawo karshen yarjejeniyar fahimtar juna a kan jibge rundunar hadaka da Amurka ke jagoranta a kasar.
Kakakin Majalisar Iraqi Mohammed al Halbousi, ya ce bai yiwuwa a dakatar da yarjejeniyar ba tare da bada wa’adin shekara guda na yin hakan ba.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bayyana shakku kan batun korar sojojin Amurka, ya fadawa labaran Talabijin na Fox cewa, ya na da kwarin gwiwa mutanen Iraqi suna so Amurkawan su ci gaba da zama a wurin.
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Morgan Ortagus, ta ce Amurka ta yi nadama da wannan shawarar Iraqi kuma tana jira ta samu karin bayani a kan batun barin kasar a dokance. Ta ce Amurka tana kira ga Iraqi da ta sauya tunaninta.