Majalisar Dokokin Uganda ta Fidda Dokar dake Kayyade Shekarun Takarar Shugaban Kasa

Majalisar Dokokin Uganda

Majalisar dokokin kasar Uganda ta kada da wata kuri’ar fidda kayade yawan shekaru ga masu shiga takarar shugabancin kasa da gagarumin rinjayi, domin bada dama ga daya daga cikin dadaddeun shugabannin Afrika ya ci gaba da mulki har izuwa shekarar 2031.

Kuru’u 315 na masu ra’ayin shugaban ya zarce a kan kuru’u 62 na wadanda basu ra’ayin hakan, ya kai ga yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska ta yanda za a fidda matakin dake hana matasa yan shekaru 35 ko kuma tsofaffi masu shekaru 75 zama shugaban kasa.

Karkashin dokar ta yanzu, shugaba Yoweri Museveni mai shekaru 73 ba zai iya shiga takarar zaben shugaban kasa a shekarar 2021.

Kudurin zai zama doka da zarar Museveni ya sanya hannu a kai.

Sabon kudurin dokar ya kayyade wa’adin shugabancin kasa, amma zai fara aiki ne bayan zabe mai zuwa, wanda zai baiwa Museveni daman yin wasu wa’adin shekaru biyar sau biyu.

Galibin yan Uganda sun yi amfani da kafafen sada zumunta suka bayyana nadamarsu ga tabbatar da wannan kuduri. Yau bakar rana ce kuma komawa baya ne ga wani bala’I inji Mwanmbutsye Ndebesa wani masanin tarihin siyasa a wata jami’ar Uganda ta Makerere. Yace bai ga wani Alheri tattare da wannan matakin ba.