Cikin tsauraran matakan tsaro Majlisar Dokokin Nijar ta yi zamanta jiya Lahadi inda aka girke jami'an tsaro a duk hanayar da ta shiga Majalisar.
To sai dai hayaniya ta barke a zauren Majalisar tsakanin shugaban Majalisar da bangaren adawa saboda zargin da 'yan adawan suka yi masa na nuna bangaranci a lokacin da suke muhawara.
Ministan kudi Hassan Masaudu ya yiwa 'yan Majalisar bayani domin kare hujjojin gwamnati wajen bullo da sabbin haraji wadanda galibinsu matakai ne da ministan ya ce na dede da tsarin harajin bai daya na kasashen kungiyar IRMUWA kafin ya amsa tambayoyi akan wasu matakan da ake gani za su iya jefa talakawa cikin kunci.
A cewar ministan duk abun da aka yi saboda talakawa ne domin an sa za'a gina hanyoyi, a bada ruwa, a kyautata harkokin kiwo da noma da samar da tsaro. Yana ganin kururuwar da 'yan adawa ke yi duk shirme ne.
A karshen muhawarar 'yan Majalisar sun amince da kasafin da kur'u dari da talatin da uku daga cikin dari da saba'in da daya, ke nan talatin da takwas kacal ne suka ki amincewa.
Gwamnatin na sa ran kashe sefa biliyan dubu daya da dari takwas a kasafin kudin badi abun da 'yan adawa suka lashi takobin ci gaba da gwagwarmaya a kansa
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5