Majalisar Dokokin Najeriya Zata Yi Gyara-Gyare A Kundin Zaben Kasar

Majalisar dokokin Najeriya ta ce gyare-gyare fiye 80 zata gudanar a kudin dokar zaben kasar wanda za’a kammala cikin watanni uku masu zuwa. Sai dai masu nazarin harkokin zabe a kasar na cewa akwai bukatar ilimantar da ‘yan najeriya kafin aiwatar da gyare-gyaren.

Fiye da shekara 10 kenan majalisar dokokin ta Najeriya ba ta yi aikin gyaran kundin zaben ba, wanda ya kamata a rinka dubawa duk bayan shekara hudu. Sai dai a wannan karon majalisar ta dukafa domin ganin ta sauke wannan nauyi kafin zaben shekarar 2023.

Sanata Ibrahim Shekarau, da ke kwamitin majalisar dattawa kuma mai kula da ayyukan hukumar zabe ta INEC, ya ce an kafa kwamitin fasaha tsakanin ‘yan majalisu na ayyukan hukumar zaben ta INEC, wanda zai yi zama na musamman, kafin ya mika wa majalisa dukkan gyare-gyaren da ya yi.

Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa na Jami’ar Bayero Kano, ya fayyace alfanun gudanar da gyare-gyare a kundin zaben kasar ta Najeriya, inda ya ce abubuwa da yawa sun faru tun lokacin da aka yi wa kundin tsarin zaben kasar kwaskwarima, alal misali an samu tashe-tashen hankula lokacin zaben shekarar 2011, to kamata ya yi a zauna a gano me ya janyo irin wannan matsalar, amma ba a yi ba.

Sanata Masʽud El-Jibril Doguwa, tsohon wakili a zauren majalisar dattawan Najeriya, ya ce kamata ya yi majalisun Najeriya su zauna su fito da dukkan bangarorin da jama’ar kasar ke korafi a kansu, misali kamar maganar Inconclusive, su ji menene ra’ayoyin mutane, idan akwai gyara to su gyara.

Sabon daftarin zaben shi ne zai fayyace yadda zaben Najeriya zai gudana a shekara ta 2023.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dokokin Najeriya Zata Yi Gyara-Gyare A Kundin Zaben Kasar