Majalisar Dokokin Najeriya Ta Amince Da Dokar Ba Yan Kasa Damar Tsayawa Takara Na Kashin Kai

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Ibrahim Abdullahi Gobir

Majalisar dokokin Najeriya ta amince da dokar da za ta ba yan kasa damar tsayawa takara na kashin kai. Tuni an mika dokar ga shugaban kasa domin ya rattaba mata hannu ta zama doka.

Daga dukan alamu dokar ta samu karbuwa domin yan majalisar sun ce dokar ba ta su ba ce, ta yan kasa ce.

Wannan doka da majalisa ta gabatar ita ce dokar sauya Kundin tsarin mulki mai lamba 58, wacce a yanzu haka ta samu amincewar Jihohi 31 daga cikin jihohi 36 na kasar wanda ya nuna cewa an samu kashi biyubisa uku na yawan jihohin da ake so su amince da dokar kafin ta zama doka.

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Ibrahim Abdullahi Gobir ya yi karin haske cewa wannan doka za ta yi tasiri sosai a kasar domin za a kai faggen da wanda duk mutane ke so shi za su zaba.

Saboda haka ba dole bane sai mutum ya tsaya a karkashin Jamiyya, domin ya nuna cewa an ba yan siyasa yanci kuma don haka yana da kyau sosai.

Gobir ya ce ba wai 'Yan Majalisa ne suka kawo dokar ba, Yan Kasa suka kawo dokar kuma Majalisa ta yi aikin ta. Gobir ya ce dokar tana cikin Dokokin 44 da Majalisar Kasa ta riga ta yi gyara akan su, kuma an samu amincewar Kashi biyu bisa uku na jihohin kasar 36, saboda haka an aika wa Shugaban Kasa dokar domin ya sa mata hannu.

Shi ma mataimakin Mai tsawatar wa a Majalisar dattawa Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya kara jadadda hujjar amincewa da dokar da sharudan da dokar ta kunsa.

Sabi ya ce ba haka kawai dokar ta zo ba, an lura cewa idan ba a sa sharuda ba, mutane za su fito da yawa, su ruda tsarin, tareda yi masa karan tsaye.

Sabi ya ce sai mutum ya samu yawan adadin wadanda za su sa masa hannu a lokacin tsayawar sa takara, wanda shi ne zai taimakawa Hukumar zabe wajen yin aikin ta na tantancewa.

A lokacin da yake nazari akan wannan batu na samun dokar da dan siyasa zai iya tsayawa takara, Kwararre a fanin siyasa kuma malami a Jami'ar Abuja Dokta Abu Hamisu ya ce abin murna ne samun wanan doka ganin cewa tuni kasashen da suka cigaba suna aiwatar da ita. Abu ya ce a nan Najeriya, dokar za ta ba da dama a samu mutane wadan da suke son sauye sauye a yanayin mulki. Abu ya ce zai rage yawan koran mutane a jamiyyu barkatai babu adadi saboda kawai mutum ya bayyana ra'ayin sa.

Kudirin ya tanadi cewa duk wani dan Najeriya da ya ke so ya tsaya takarar shugaban kasa a matsayin dan takara mai zaman kansa, dole ne ya samu sa hannun da aka tantance na akalla kashi 20 cikin 100 na masu kada kuri’a daga kowace jiha ta tarayya. Haka ya ke a takarar Gwamna a jihar sa, da na Yan majalisu da ma shugabanin kananan hukumomi.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

INDEPENDENT CANDIDACY---NASS PASSES BILL , READY FOR PRESIDENTIAL ACCENT.mp3