Majalisar Dokokin Masar Ta Amicewa Al-Sisi Ya Tura Sojoji Libya

Majalisar dokokin Masar ta baiwa shugaba Abdel Fattah al-Sisi dama ya kai gudunmuwar sojojin kasar a makwabciyarta Libya idan bukatar hakan ta taso.

A farkon wannan wata ne al-Sisi ya yi kashedi ga gwamnatin Libya da ke birnin Tripoli da masu goya mata baya a Turkiya cewa, su yi taka tsantsan kada su wuce gona da iri, abin da ya bayyana mai muhimmanci ga tsaron Masar a birnin Sirte na Libya mai tashar jirgin ruwa.

Kuri’ar da aka kada a majalisar dokokin Masar a kan Abdel Fattah al-Sisi a kan ya dau mataki a Libya, ba ta nuna fara ayyukan soji nan da nan a kan dakarun abokan gaba a Libya ba.

A halin da ake ciki, kafafen yada labaran Masar sun ce al-Sisi ya zanta da shugaban Amurka Donald Trump ta wayar tarho da yammacin ranar Litinin, tattaunawar da ta maida hankali a kan tsagaita wuta a Libya domin dakile barnar da ke faruwa.

Majalisar dokokin a gabashin Libya ta fitar da wata sanarwa a makon da ya gabata, ta bada dama Masar da ke goyon bayan gwamnatin wucin gadi ta Abdallah al Thini a gabashin Libya, ta kawo mata gudunmuwar soji, idan bukata ta taso, ganin yadda Turkiya ta shiga dumu dumu cikin Libya kana taki mutunta ‘yancin kasar.