Majalisar Dokokin Libya ta Rantsar da Gwamnatin Firayim Minista al-Thani

Firayim Ministan Libya Abdullah al-Thani

A kokarin kare kasar Libiya daga rugujewa majalisar dokoin da duniya ta amince da ita ta rantsar da gwamnatin firayim ministar kasar

Majalisar dokokin kasar Libya da kasashen duniya suka amince da ita ta rantsar da gwamnatin Firai Minista Abdullah al-Thani jiya Lahadi, yayinda Majalisar Diniki Duniya ake kokarin ceto kasar daga rugujewa.

Gwamnatin Thani tana da zama a birnin Tobruk.Ta kaura zuwa wurin ne watan da ta gabata bayanda mayakan kishin Islama daga birnin Misrata suka kwace Tripoli babban birnin kasar, suka kafa gwamnatinsu da kuma majalisa.

Majalisar Dinkin Duniya ta gayyaci wakilan banbagorin biyu domin tattaunawa yau Litinin kusa da kan iyakar Algeriya, sai dai babu tabbacin wanda zai halarci zaman.