Kasar Nijar na yankin da masana harkokin tsaro suka bayyana na da mahimmanci wajen daukan matakan karya lagon kungiyoyin ta'addancin da suke cikin kasashen yankin Sahel.
Mahimmancin ya ba da hujjar kafa sansanonin dakarun kasashen yammacin Turai a Nijar da makwafciyarta Mali. Shi ne kuma mafarin da ya sa Majalisar Dokokin Jamus ta aika da tawaga Nijar domin tattaunawa akan harkokin tsaro.
Onarebul Hamma Asan shugaban kwamitin majalisar dokokin Nijar dake kula da harkokin tsaro yace ba Nijar ko kasashen Sahel ne kawai ba ke fama da tsaro da ayyukan ta'addanci. Yana mai cewa harkokin tsaro sun shafi duka al'ummar duniya. Kowa na jin abubuwan dake faruwa a kasashen Spain, Faransa da duk kasar da 'yan ta'adda suka kunno kai.
Onarebul Hamma yace yanzu lokaci ya yi da duk kasashe, kama daga Afirka zuwa Turai, zasu hada kawunansu su yaki wannan bala'i tare domin a fita daga ta'addanci.
Samun labarai akan halin da sojojin Jamus ke ciki a bakin daga na cikin dalilan da tawagar ta Jamus ke ziyartar Nijar, musamman majalisa. Akwai sojojin Jamus da kayan aiki irin na zamani suna aiki kafada da kafada da sojojin Nijar a Agadez. Burin kasashen biyu dangane da kokarin murkushe ta'addanci ya zo daya.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5