Majalisar Dokokin Isra'ila Ta Amince Da Dokar Wanene Dan Kasa.

Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Da safiyar yau Alhamis, majalisar dokokin Isra'ila ta amince da wata doka mai cike da takaddama, cewa yahudawa ne kadai a kasar suke da 'yanci ikirarin zama 'yan kasar, dokar ta kuma karfafa kafa sansanonin 'yan share wuri zauna.

Dokar mai ikirarin diyauci wakilai 62 ne suka amince da ita yayinda 55 suka ki, bayan da aka shafe sa'o'i takwas ana zazzafar muhawara da suka, musamman daga wakilai larabawa a majalisar.

Wasu wakilai larabawan cikin fushi suka yage dokar, suka ce da kafa wannan doka, "demokuradiyya ta mace" kuma an kai wani "mizani" na wariya a Isra'ila.

Amma PM Benjamin Netanyahu, ya jinjinawa dokar, a zaman muhimmi a tarihin kafawa da habaka kasa ta bai Yahudu