Matakin garkame masu adawa da dokar harajin kasar Nijar ta 2018 a wasu gidajen yari ba tare kotu ta yanke masu hukumci ba, shine abun da ya dauki hankalin majalisar dokokin kasar Faransa, kasar da ta yiwa Nijar mulkin mallaka.
Majalisar ta bukaci shugaban Faransan Emmanuel Macron ya yi amfani da ziyarar shugaban Nijar din Issoufou Mahammadou a kasar Faransa, ya sanar dashi cewa matakin ya sabawa tsarin Dimokradiya.
A cewar Inusa Jimrau, babban sakataren kungiyar NPCR, shugaban majalisar dokokin Faransa da ya kai ziyara Nijar ya ja hankalin ‘yan majalisar akan abubuwan da ya gani a Nijar. Yayi kira ga shugaban Faransa Macron, ya san cewa abokinsa shugaban Nijar da yake ikirarin dan Dimokradiya ne ba haka yake ba. Yana karya hakkin dan Adam, kuma babu Dimokradiya a Nijar, tsarin ya gurgunce a kasar.
Kazalika wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa sun shirya gabatar wa shugabannin kasashen biyu, Faransa da Nijar, wata kasida a yammacin talata, dake bukatar a saki duk wadanda hukumomin Nijar suka kama saboda dalilan gudanar da zanga zanga, inji Kaka Tula Gwani, na wata kungiyar kare hakkin dan Adam. Y ace wasikar da zasu gabatar mutane fiye da dubu uku daga kasashe daban daban suka sa hannu. Ya ce yau fiye da kwana sittin ke nan da Nijar ke tsare da mutane 26.
A ranar 25 ga watan Maris ne hukumomin Nijar suka cafke shugabannin kungiyoyin dake adawa da dokar harajin 2018 saboda zarginsu da gudanar da zanga zanga ba tare da iznin hukuma ba.
Amma kakakin gwamnati y ace “ idan gwamnati dake da hakkin tsaro da kiyaye lafiyar al’umma ya ga akwai wani cikas da ka iya wakana a kasar ta fito ta hana a yi zanga zangar, ai sai a yi hakuri a yi gaba”
Shugaban Nijar Muhammadou Issoufou yana Faransa ne domin tattaunawa da takwaransa akan yadda za’a inganta wutar lantarki a Nijar tare da yaki da ta’addanci.
A saurari rahoton Souley Mummuni Barma
Your browser doesn’t support HTML5