A baya dai shugaba Muhammadu Buhari ya ki sa hannu kan kudurin dokar sauya fasalin zabe da Majalisar Dokoki ta aika masa. ‘Yan Majalisar dai sunso a yi zabensu ne da na gwamnoni da farko, sabanin yadda hukumar zabe ta zayyana jaddawalin zaben.
Dokar ta janyo cece-kuce tsakanin fadar shugaban kasa da Majalisar, domin wasu sassa da shugaba Buhari ya ce bai amince da su ba.
Shugaban kwamitin kula da harkokin zabe Sanata Sulaiman Nazif, ya ce sun riga sun kammala aiki akan fannonin da shugaba Buhari bai amince da su ba,
Idan har shugaba Muhammadu Buhari ya amince ya sa hannu a wannan kuduri, to zata shiga jerin dokokin zabe. kuma za a fara zaben shekara ta 2019 da zaben shugaban kasa kafin a yi na gwamnoni da na ‘yan Majalisu.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Medina Dauda.
Your browser doesn’t support HTML5