Majalisar Dokoki Bata Da Hurumin Binciken Badakalar Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin haramtawa majalisar dokokin jihar, gudanar da binciken faifen bidiyon dake zargin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, yana karbar rashawar Dala Miliyan biyar daga wasu ‘yan kwangila.

Wata kungiyar lauyoyi mai rajin wanzar da tsarin mulkin demokaradiyya a Najeriya, Lawyers for Sustainable Democracy in Nigeria ta shigar da kara gaban kotun a watan jiya, tana kalubalantar hurumin majalisar na bincikar wannan batu.

Matakin kungiyar ya biyo bayan kwarmaton da jaridar Daily Nigerian tayi ne wadda ta yada bidiyon mai dauke da hoto da kuma muryar gwamna Ganduje, yana karbar wadancan miliyoyin dala da tace ‘yan kwangila suna bashi.

Bayan wannan kwarmato majalisar dokokin ta Kano ta kafa wani kwamiti mai wakilai biyar domin binciko sahihanci ko akasin wannan zargi.

To amma kungiyar Lauyoyin masu rajin wanzar da demokaradiyya a Najeriya tace majalisar ba ta da hurumin yin hakan, lamarin daya sanya ta garzaya gaban babbar kotun Kanon.

A zaman kotun na yau karkashin jagorancin Justice Ahmad Tijjani Badamasi, tace majalisar bata da hurumin gudanar da bincike kan irin wannan zargi, yana mai cewa, hukumar ‘yan sanda da hukumomi yaki da rashawa na EFCC da ICPC ne kawai keda wannan hurumi.

Kotun ta kuma haramtawa jaridar Daily Nigeria ci gaba da yaya ta wancan faife na bidiyo ta kowace irin siga, tana mai cewa, kamata ya yi tun fari shi mawallafin wannan jarida Jafa Jafar ya mika wannan faifen ga hukumar ‘yan sanda ko kuma hukumomin ICPC da EFCC.

Barr Mohammed Zubair shine shugaban kungiyar Lauyoyin data shigar da wannan kara. To amma shugaban kwamitin da majalisar dokokin ta Kano ta kafa mai binciken wannan zargi akan gwamna Ganduje Hon. Baffa Babba Dan-Agundi na cewa.

Gabanin wannan hukunci, kimanin makonni biyu da suka gabata, gwamanan na Kano ya gurfanar da mawallafin jaridar Daily Nigerin, data kwarmata wancan bidiyo a gaban babbar kotun Kano, yana neman diyyar naira biliyan dubu uku daga hannun Ja'afar Jafar saboda bata masa suna.

Ga rahoton wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Mahmu Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dokoki Bata Da Hurumin Binciken Badakalar Ganduje 2'30"