Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya amince da korar duk wani wanda aka samu da hannu cikin zargin aikata cin zarafin saduwa a lokacin da sojoji ke ayyukan kiyaye zaman lafiya a kasashen duniya.
Bangaren Majalisar sulhu na MDD ya zabi rungumar kundin hukunta laifuffukan da Amurka ta fitar a matsayin a matsayin na wucin gadin da za a iya bitarsa don yin gyara sannan a yi amfani da shi don yin hukunci.
Jakadar AMurka a MDD Samantha Power ta kara da cewa, “Wannan mataki ya nuna a fili cewa aikinmu mu dau matakin da ya dace ga duk wanda aka samu da laifin cin zarafin mata da yara da sunan kiyaye zaman lafiya.
Shima jakadan Birtaniya a MDD cewa yayi, wannan magana ce ta gaggauta daukar matakin da ya dace akan wannan babban zargin laifi na cin zarafi ta inda bai kamata ya bullo ba.