Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya sabunta wa’adin aikinsa na tabbatar da zaman lafiya a Sudan Ta Kudu da tsawon shekaru guda, sannan ya yi gargadin cewa muddun aka cigaba da yaki to zai kakaba takunkumin sayo makamai.
Bayanin, wanda Amurka ta jagoranci rubutawa, ya bayyana, abin da ya kira, “shirin kwamitin na daukar duk wani matakin da ya dace, kan masu aikata abubuwan da ke kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma tsaron kasar Sudan Ta Kudu”
Jakadan Sudan da Kudu ya bayyana matakan ladabtarwar da ci-baya.
“Wani abu ne dabam a yi tir da tsarin shugabancin kasa, sannan wani abu ne kuma dabam a yi barazanar kakaba ma ta takunkumin sayo makamai, wanda, kamar yadda na gaya ma kwamitin tun farko, babu abin da zai haifar illa rashin jituwa da kuma tabarbarewar lamarin.
An yi ta gwabza fadan kabilanci da kuma yakin basasa tsakanin sojojin da ke biyayya ga Shugaba Salva Kiir, da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Riek Machar.
An kasa aiwatar da yarjajjeniyar zaman lafiyar da aka cimma a watan Disamba.