Shugaban kwamitin na majalisar dinkin duniya Zeid Ra’ad Al Hussein, yace har yanzu ana ci gaba da zaman dar dar, kuma har yanzu ana ci gaba da tashin hankali a babban birnin Juba da sauran sassan kasar. bayan binciken fadan har na tsawon kwanki biyar, wanda ya fara ranar 7 ga watan Yuli.
A wani rahoto da aka fitar wannan makon, kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya, yace yana da bayanan akalla 217 na fyade da ya faru a Juba, tsakanin 8 ga watan Yuli zuwa 25 ga watan Yuli.
Mata daga kabilu daban daban sun fuskanci cin zarafin fyade daga sojojin Sudan ta Kudu. Rahotan na nunin cewa yawanci yara matasan da ke dauke da makamai ne suka aikata wannan danyen aikin wadanda akayi imanin cewa suna da nasaba da sojojin SPLA,Yawancin abinda da rahoton ya bayyana shine sojojin gwamnati ne suka aikata wannan aika-aikan.
Rahoton wanda aka mikawa kwamitin tsaron ya bayyana cewa yawancin wadanda aka yi wa wannan cin zarafin yara ne kanana
Sama da mata da yara 100 ne suka ce anyi musu fyade akan hanya fita daga birnin Juba zuwa Yei, bayan da tashin hankalin ya fara kwantawa.
Shaidu da kuma wadanda abin ya faru da su sun fadawa ma’aikatan kare ‘yancin dan adam cewa, Sojoji sun kwacewa mata da yara kayayyakinsu har ma da yi musu duka a wajen shingayen da jami’an tsaro ke duba masu wucewa.