Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya game da Somalia da Muriyar Amurka ta samu yace cin hanci da rashawa ya ratsa ta ko ina cikin gwamnatin wucin gadi a Somalia har aka lakabawa cuwacuwar inkiyar “nawa ne rabo na a ciki”.
Wani kwamitin sa ido kan Somalia da Eritrea da Somalia yace tsagwaran satar dukiyar gwamnati ta sa wadansu ‘yan siyasa suke neman yin makarkashiya ga shirin zabe a kasar.
Wa’adin goyon bayan da Majalisar Dinkin Duniya take baiwa Somalia zai kare a karshen watan Agusta mai zuwa. Majalisar Dinkin Duniya da Amurka, da Tarayyar turai ne suke samar da galibin kudaden gudanarwa na gwamnatin Somalia.
Rahoton yace kashi 70 cikin dari na gudumawar kudi da aka baiwa kasar baya shiga baitul malin gwamnati ba a 2009 da kuma 2010.
Haka kuma rahoton yace rubu’i na kusan kudaden gwamnati da aka kashe a bara kamar dala miliyan 12, an kashe su ne a ofishin shugaban kasa Sheikh Sharif Sheikh Ahmed, da ofishin PM Abdiweli Mohammed Ali, da kakakin majalisa Sharif Hassan Adan.
Sai dai ofishin Firai Mimista yayi watsi da rahoton da cewa karya ne tsagwaran.