A nata bangare hukumar yan gudun hijira ta kasar Norway ta fitar da wata kididdiga a ranar Litinin, cewa kimanin mutane miliyon biyar da dubu dari biyu ne da tarzomar Boko Haram ta daidaita ke fuskantar barazanan yunwa.
Hadimin mukadashin shugaban kasar Nigeria Alhaj Hafizu Ibrahim yace ofishin na farfesa Osinbajo yana daukar mataki a kan wannan lamari. Yace a baya mukadashin shugaban kasar ya je Maiduguri inda ya kaddamar da shirin bada abinci ga yan gudun hijira kana yayi alkawari cewar za'a bi yan gudun hijira a inda suke a kai musu abinci saboda inganta sabon tsarin raba abinci.
Shi kuwa babban kwamandan rundunar yaki da Boko Haram a kasashen yankin tabkin Chadi Manjo Janar Leo Irabo ya nuna matukar damuwansa da irin wannan alkaluma masu ban mamaki da kasashen turawa ke bayarwa a kan Nigeria. Yace ya kamata hukumomin gwamnatin Nigeria su yi aikin samar da irin wadannan alkaluma.
Your browser doesn’t support HTML5